18 Maris 2022 - 18:59
Kasashen Iran Da Siriya Za su Fadada Dangankatarsu A Bangarorin Man fetur Da Albarkatun Kasa

Manyan jami’an diplomasiyar kasashen Iran da siriya sun tattauna game da hanyoyin da za’a bi wajen fadada dangantakar dake tsakaninsu musamman a bangaren manfetur da kuma sauran albarkatun kasa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ganawar da ta gudana ne a birnin Demaskas na kasar siriya tsakanin ministan mai da Albarkatun kasar na siriya Bassam Tuhme da mai bawa minsitan tsaron kasar iran shawara Mostafa Ebati wanda shi ne shugaban cibiyar kasuwanci ta hadin guiwa tsakanin kasashen biyu.

Kamfanin dillancin labaran kasar Siriya Sana ya nakalto cewa jami’an kasashen biyu sun tattauna game da yarjejeniayr fahimtar juna da aka sanya hannun a kai tsakanin Tehran da Damaskas da ta kun shi bangorin manfetur da iskar gas kayyakin aki da butut da kuma Naurorin hako man fetur

Har lila yau wakilin kasahen biyu sun jaddada cewa da sannu za’a fara aiki da dukkan yarjeniyoyin da aka rattaba hannu a kai tun a baya, da zai taimaka wajen kara bunkasa dangantakar tattalin arziki dake tsakaninsu.

342/